Tope Ademiluyi
Appearance
Tope Ademiluyi | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Tope (mul) |
Shekarun haihuwa | 23 ga Augusta, 1965 |
Yaren haihuwa | Yarbanci |
Harsuna | Turanci, Yarbanci da Pidgin na Najeriya |
Writing language (en) | Turanci |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | gwamnan jihar Ekiti |
Ɗan bangaren siyasa | Peoples Democratic Party |
Ƙabila | Yaren Yarbawa |
Adetope Ademiluyi (an haife shi a ranar 23 ga watan Agustan 1965) ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon muƙaddashin gwamnan jihar Ekiti.[1]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]Ademiluyi daga Aramoko-Ekiti, Ekiti-West, Jihar Ekiti.[2]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya karɓi muƙamin muƙaddashin gwamna a jihar Ekiti a ranar 27 ga watan Afrilun 2007, kuma ya gaji Tunji Olurin, muƙaddashin gwamnan da ya gabata.[2] Ademiluyi ya riƙe wannan muƙamin har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2007, lokacin da Olusegun Oni ya karɓi mulki. Adetope Ademiluyi wanda tsohon ɗan jam’iyyar People’s Democratic Party ne a yanzu yana jam’iyyar All Progressives Congress Party.